Tehran (IQNA) - Kasashe da dama na duniya sun karbi bakuncin dubban jama'a a yau Juma'a wadanda suka bayyana goyon bayansu ga al'ummar Palastinu sakamakon munanan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa zirin Gaza.
An gudanar da zanga-zangar a kasashe daban-daban da suka hada da Iran, Iraki, Yemen, Syria, Lebanon, Amurka, Pakistan, da Malaysia.