IQNA

Hotunan Asibitin Gaza bayan Mummunan Bam na Isra'ila

AL-QUDS (IQNA) - Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai wani mummunan hari a asibitin al-Ahli Arab da ke Gaza a wani samame da suka kai jiya Talata da dare, inda suka kashe fararen hula fiye da 500, galibi mata da kananan yara, tare da jikkata wasu daruruwan.

Kafin kisan kiyashin, hukumomi sun bukaci mutanen Gaza da su je asibitoci domin tsira daga hare-haren Isra'ila.