IQNA

Ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falastinu a duniya

TEHRAN (IQNA) - Dubban jama'a a sassan duniya ne suka gudanar da zanga-zanga a kan titunan garuruwansu a karshen mako domin yin Allah wadai da zaluncin da Isra'ila ke yi a zirin Gaza, inda suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa.

An gudanar da zanga-zangar a kasashe daban-daban da suka hada da Amurka, Afirka ta Kudu, Brazil, Ireland, Koriya ta Kudu, Pakistan, UK, Jamus, Italiya, da Argentina.

Harin da Isra'ila ta kai tun ranar 7 ga watan Oktoba ya lakume rayukan Palasdinawa fiye da 10,000 galibi mata da kananan yara a yankin Zirin Gaza da aka yiwa kawanya.