Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Dzair ya bayar da rahoton cewa, a safiyar jiya Asabar ne aka fara gudanar da taron koyan kur'ani mai tsarki a fadin kasar a karon farko a kasar Aljeriya, tare da halartar ministan harkokin addini na kasar Youssef Belmahdi, a otal din Golden Sands dake birnin Zaraldeh.
A wajen bude wannan taro, Muhammad Hassouni mai baiwa shugaban kasa shawara kuma mai kula da harkokin addini da makarantun kur'ani a kasar Aljeriya shi ma ya halarta.