IQNA

Sheikh Zakzaky Ya Ce:

Ya fara wa’azi ne ta hanyar yin amfani da tafsirin kur’ani da bayanain ayoyinsa

19:56 - January 30, 2024
Lambar Labari: 3490563
IQNA - Jagoran Harka Islamiyya a Najeriya Sheikh ya bayyana cewa ya fara yin wa’azi ne ta hanyar yin amfani da tafsirin kur’ani mai tsarki.

Jagoran Harka Islamiyya a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky a lokacin da yake halartar wani taron karrama shi a jami’ar Almostafa a birnin Qom na kasar Iran a ranar jiya Litinin, ya bayyana cewa ya fara yin wa’azi ne ta hanyar yin amfani da tafsirin kur’ani mai tsarki da bayanain ayoyinsa.

Ya ce tun shekaru 44 da suka gabata a lokacin da yake a jami’a a Zaria, yana gabatar da jawabai na addini, kuma yana amfani da kur’ani mai tsarki wajen bayanin ayoyinsa da suke koyar da dan adam darussa.

Sannan kuma ya yi ishara da cewa, ya tashi a gidansu ana koyar da su kur’ani, domin kuwa mahaifinsa malamin kur’ani a cikin garin Zaria.

Tun a cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata ce malamin yayi tafiya zuwa Iran domin neman magani tare da matarsa, inda har yanzu yake ci gaba da karbar magani, kamar yadda kuma yake halartar taruka daban-daban da kuam ganawa da malamai da cibiyoyi a kasar ta Iran.

Haka nan kuma ya samu kyautuka daban-daban na karramawea daga jami’oi da kuma wasu cibiyoyi na gwamnati da kuma masu zaman kansu.

 

 

4196694

 

captcha