Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na J News cewa, a bana mutane 6,000 ne za su halarci taron Itikafi na wannan masallaci a cikin watan Ramadan.
Shugaban sashin jagoranci da nasiha na masallacin Abdul Mohsen Al-Ghamdi ya ce: Wannan adadi ya nuna karuwar kashi 100 idan aka kwatanta da na bara.
Al-Ghamdi ya kara da cewa: Za a ware wa mata mutum 1,000 daga kason da aka yi na itikafi.
A cewarsa, an ware hawa hawa uku na Masallacin Harami ga mahalarta taron Itikafi na bana.
Ana yin Itikafi ne a kwanaki 10 na karshen watan Ramadan.
An fara rajistar shiga masallacin Harami ne a ranar bakwai ga watan Ramadan kuma za a ci gaba da yin rajista har sai an cika karfin.
https://iqna.ir/fa/news/4206874