IQNA

An fara gasar kur'ani mai tsarki ta kasar Libya karo na 12

14:52 - May 12, 2024
Lambar Labari: 3491136
IQNA - A jiya ne aka fara gudanar da gasar haddar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na goma sha biyu a birnin Benghazi.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-Wasat cewa, a jiya Asabar ne aka fara gudanar da gasar haddar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na 12 tare da halartar sama da mutane 96 a birnin Benghazi.

An gudanar da bikin bude gasar kur'ani ta kasa da kasa karo na 12 a kasar Libiya tare da halartar firaministan kasar Osama Hammad da babban jami'in kula da harkokin Awka da Musulunci Atef Al-Obeidi tare da adadin sauran sojojin Libiya da jami'an farar hula.

Babban daraktan hukumar Awqaf ne ya shirya gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Libya karo na 12 tare da halartar sama da ’yan takara 96 ​​daga kasashe 60 na duniya.

Mahalarta gasar sun fafata a fannoni guda uku: hardar kur'ani mai girma gaba daya, da haddar tafsiri, da haddar ruwayoyi goma.

A gefe guda kuma za a gudanar da wasu gasa guda biyu a bayan wadannan gasa, wadanda suka hada da karo na biyu na gasar kimiyya da bincike na kur'ani mai tsarki da kuma matakin farko na tsarin ilimin kur'ani mai tsarki.

 

4215250

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha