A cewar jaridar Standard, an tuhumi wani mutum da laifin nuna wariyar launin fata bayan ya fesa jan fenti a wasu masallatai da kasuwannin musulmi da kuma karamin ofishin jakadancin Falasdinu da ke yammacin London.
Daga ranar 16 ga Oktoba zuwa 18 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata, wannan mutumin ya fesa fenti a wuraren Musulunci a Hammersmith, Fulham da Ealing sau 11.
Ofishin jakadancin Falasdinu da ke Hammersmith na daga cikin wuraren da aka kai harin, wanda 'yan sanda suka bayyana a matsayin "mai kyamar musulmi".
An tuhumi Jonathan Kattan mai shekaru 61 da haifuwa a kan wannan lamari, kamar yadda ‘yan sanda suka sanar a ranar Alhamis. Kattan, daga Ealing, 'yan sanda sun kama shi a ranar 27 ga Nuwamban bara.
A yanzu an tuhume shi da laifuka 11 na lalata da wariyar launin fata, da laifuka daya na wariyar launin fata a karkashin sashe na 5 na dokar odar jama'a da kuma laifin keta doka a karkashin sashe na 4 na dokar jama'a. An shirya zai bayyana a Kotun Majistare ta Uxbridge a ranar Juma'a (gobe, 17 ga Mayu).
Figo Frozan, jami'in binciken da ke gudanar da binciken ya ce: Nasarar wannan shari'ar ta samo asali ne sakamakon kwazon da jami'an 'yan sanda suka yi, inda suka tattara shaidu ta hanyar tallafawa da kuma kwantar da hankulan mutanen da suka jikkata.
Senior Constable Sean Wilson ya kara da cewa: "Rundunar 'yan sanda na ci gaba da aiki tare da Hukumar Kula da Laifuka ta Crown da al'ummomin yankunan Ealing, Hammersmith da Fulham don kamawa da gurfanar da wadanda ake tuhuma a wannan shari'ar.
Ya kara da cewa: Wannan ya nuna yadda muke daukar tuhume-tuhumen laifuffukan kiyayya ga kowace al’ummarmu.
Wilson ya jaddada "Yayin da ake ci gaba da gudanar da shari'ar laifuka a halin yanzu, ina kira ga al'umma da su guji yin cece-kuce game da wannan lamari, musamman a shafukan sada zumunta domin kaucewa duk wani son zuciya."