Daga nan sai karatun ayoyin kur’ani tare da Ghasem Moghadami, makarancin kasa da kasa na kasar Iran
An ci gaba da gudanar da taron tare da karatun Raudah tare da Morteza Taheri, babban malamin Ahlul Baiti (AS) a wajen zaman makokin Ayatullah Raisi da tawagarsa.
Hamidreza Ahmadiwafa, makarancin kasa da kasa na kasar Iran ya karanta ayoyi a cikin suratul Rahman.
Bayan haka, Hojjat al-Islam Nasser Rafiei, farfesa na Jami’a da Hauza, ya gabatar da jawabi.
Ya yi nuni da abin da ke cikin ziyarar hajjin Aminullah ya ce: Ya Allah mun amince da duk abin da ka tsara da hukuncinka, kuma mun natsu.
Jagoran juyin juya hali ya ce, mun rasa manyan jiga-jigai, amma kuma ba za mu ja da kaddara ta Allah ba, muna kuka amma ba korafi ba, Domin kuwa Abin da ya faru na ibtila’i ga Manzon Allah (SAW) ba a taba jarabtar wani dan adam da shi ba, domin shi ne mafi daraja da daukakar matsayi a wajen Allah, a kan haka jarabawarsa tafi ta kowa, kuma da shi muke koyi wajen jurewa jarabawa da ubangiji, domin manzon Allah shi ne babban abin koyi ga dukkanin masu imani.