IQNA

Halartar masu ibada kusan miliyan 8 a cikin mako guda a Masallacin Annabi (SAW)

15:52 - June 03, 2024
Lambar Labari: 3491273
IQNA - Hukumar kula da masallacin Nabiyyi da Masjid al-Haram sun sanar da halartar masallatai da mahajjata sama da miliyan bakwai da dubu dari takwas a Masallacin Annabi (SAW) a cikin makon da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ughtal cewa, hukumar kula da Masallacin Annabi (SAW) da kuma na masallacin Harami sun sanar da halartar masallata da mahajjata sama da miliyan 7.8 a masallacin annabi a cikin makon da ya gabata.

Al-Masjid Al-Haram da Masjidul-Nabi sun fitar da wani rahoto kan halartar masallatai da mahajjata a masallacin nabi inda suka sanar da cewa a cikin makon da ya gabata, mahajjata 550,960 ne suka sami karramawar kasancewa a masallacin nabi. Sama da alhazai 304,519 maza da mata ne suka gudanar da sallah a garin na Rouza Sharif.

Bugu da kari, tsofaffi da nakasassu 13,436 ne suka amfana da ayyukan da aka ware musu a makon jiya. Haka kuma, adadin masu amfani da ayyukan sadarwa a cikin harsuna da dama ya kai mahajjata 30,3869 daga kasashe daban-daban, kuma an ba da kyauta ga mahajjata maza da mata 177,549.

A cewar hukumar kula da masallacin al-Haram da masallacin Nabi, sama da mahajjata dubu 316 da 117 sun yi amfani da hidimomin jagoranci na fili sannan mahajjata dubu 69 da 221 sun yi amfani da harkokin sufuri a masallacin. Haka zalika an raba sama da kwalaben ruwan zamzam 136,800,000 da abinci 216,520 a Masallacin Annabi (SAW).

 

4219675

 

 

 

 

captcha