Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arabi cewa, Shamsuddin Hafiz mai kula da babban masallacin birnin Paris ya fuskanci wani gagarumin hari daga wannan zauren saboda goyon bayan da yake bai wa Palastinawa da kuma sukar da yake yi na kawancen ‘yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi na yahudawan sahyoniya.
A baya-bayan nan, Shamsuddin Hafiz, a yayin da yake bayyana mamakin irin bakon kawancen da jam'iyyu masu tsatsauran ra'ayi da yahudawan sahyuniya suka yi da musulmi, ya yi Allah wadai da wadannan ayyuka tare da bayyana goyon bayan sa da na al'ummar musulmi ga Rima Hassan, 'yar gudun hijirar Falasdinu kuma mai fafutuka a zaben majalisar dokokin Turai daga. jam'iyyar Faransa.
A karon farko a ranar 23 ga watan Mayu mai kula da babban masallacin birnin Paris, wanda ake yi wa kallon daya daga cikin tsofaffin masallatai mafi girma a nahiyar Turai, ya bukaci Musulman Faransa da su kada kuri'a a zaben da za a yi a Turai a ranar 9 ga watan Yuni mai zuwa. Ya nanata cewa shigar musulmi a zabubbukan "amsa ne ga rashin hakuri da kuma kyamar kansu".
Ya jaddada cewa: Babban masallacin birnin Paris ya yi kira da a yi tattaunawa tsakanin dukkanin addinai, zaman lafiya da zaman tare tsakanin addinai, al'adu da wayewa. Muna da haɗin gwiwa da yarjejeniya tare da cibiyoyi da yawa waɗanda ke yin aikinsu bisa waɗannan ka'idodin; Amma ba sabon abu ba ne a rika kai wa hari ko kalaman batanci, domin muna aiki kuma muna kan gaba a fagen siyasa kuma muna yanke hukunci mai tsauri.
A cewar Hafiz, ba za a iya daukar matakan da suka dauka na babban masallacin birnin Paris don kara tasirin addinin Musulunci ba, mu ba kungiya ba ne ko kungiyar 'yan tawaye, amma muna gudanar da ayyukanmu ne a karkashin dokokin gwamnatin Faransa da kuma hadin gwiwar hukumomin gwamnati, kuma gwamnati kuma ta amince da mu kuma ta yaba da aikinmu
Har ila yau ya jaddada cewa: A hakikanin gaskiya lamarin Gaza ba a Faransa kadai yake ba, har ma a Turai da ma duniya baki daya. Mutanen da suka kasance suna magana a kan kyawawan halaye, hakkin dan Adam da kimar dan Adam, amma a yau sun fito fili suna kare kisa; To amma a daya bangaren, akwai ’yan siyasa da kafafen yada labarai da al’adu wadanda har yanzu suke bin ka’idojinsu da dabi’unsu, kuma muna cudanya da su kuma muna neman mafita daga wannan rikici.