IQNA

Sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci ga mahajjatan Baitullahi Al-Haram:

A shekarar bana baya ga wurin aikin hajji a ci gaba da nuna bara’a a duk sassan duniya

18:21 - June 14, 2024
Lambar Labari: 3491336
A wani bangare na sakon da ya aike ga mahajjatan Baitullahi Al-Haram, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: Ya kamata a ci gaba da gudanar da tarukan nuna bara’a na bana fiye da lokacin aikin Hajji da Mikat a kasashe da garuruwan da musulmi ke da yawa a duniya.

A shekarar bana baya ga wurin aikin hajji a ci gaba da nuna bara’a a duk sassan duniya

Kamar yadda majiyar yada labarai ta ofishin kiyayewa da wallafa ayyukan Ayatollah Khamenei ke cewa, wani bangare na sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa alhazan Baitullahi Al-Haram dangane da isar da ranakun aikin Hajji. shine kamar haka:

- Babban taro da ayyukan Hajji, idan aka gan shi da idanu, abin da ke karfafawa musulmi karfi da kwarin gwiwa ne, kuma abin ban tsoro da firgici ga makiya masu mugun nufi a kan musulmi.

- Ya kamata a ci gaba da nuna bara'a a wannan shekara bayan lokacin aikin Hajji da miqat a kasashe da garuruwan da musulmi suke da su da kuma a duk fadin duniya, da dukkanin al'ummomi.

Kai dan uwa mahajjaci, yanzu kana cikin wannan fagen aiki da wadannan ilmomi madaukaka da aikin ke koyarwa. Kawo tunanin ka da aikin ka kusa da shi, kuma ka koma gida dauke da wannan kyawan halaye da akin yake koyarwa. Wannan shi ne abin tunawa kuma tsaraba na tafiyarka aikin Hajji.

 

4221401

 

 

captcha