Kamfanin dillancin labaran Anatoly ya bayar da rahoton cewa, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana a jawabin nasa cewa, nuna kiyayya tsakanin al’ummomi ba shi da wani alfanu a dukkanin bangarori na rayuwar zamantakewa, don haka tilas ne dukkanmu mu yi kokarin kawar da ita gaba daya.
Ya wallafa wadannan kalaman ne a cikin wani sako a ranar yaki da kalaman kiyayya ta duniya.
Yayin da yake jaddada cewa kalaman nuna kiyayya alama ce ta nuna wariya, cin zarafi, tashin hankali, rikici har ma da laifuffukan cin zarafin bil Adama, Guterres ya bayyana cewa an ga tasirin kalaman kyama a Jamus na Nazi da Ruwanda da Bosnia da dai sauransu.
Ya kara da cewa, a halin yanzu ana jin kalaman nuna kyama na cin zarafin al’ummomi daban-daban, wadanda galibi suna da danganta da kabilanci, addini, bangaranci ko siyasa.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya ci gaba da cewa, bisa dokokin kasa da kasa, wajibi ne kasashe su kiyaye, kuma su hana duk wani aiki na tunzura jama'arsu da kuma samar da fahimta da hadin kai a cikin al'ummominsu.
Guterres ya bayyana cewa, gabatar da dabaru da tsare-tsare na Majalisar Dinkin Duniya na yaki da kalaman kyama, wani tsari ne na magance musabbabi da illolin wannan matsala.