Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, Sami Abu Zuhri daya daga cikin jagororin kungiyar Hamas ya jaddada cewa gwamnatin sahyoniyawan na ci gaba da kashe al’ummar Palastinu, inda ya kara da cewa babu wata tangarda ko cikas ga wannan kashe-kashen.
Ya yi gargadi game da ci gaba da laifuffukan da yahudawan sahyoniya suke yi kan Falasdinawa, yana mai cewa ci gaba da kashe fararen hula a Gaza da Isra'ila ke yi zai iya haifar da kona yankin.
Wannan babban jami'in Hamas ya kuma kara da cewa: Ana ci gaba da kiraye-kirayen a tsagaita bude wuta da kuma sakin fursunonin.