Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Babban daraktan kula da harkokin al'adu na karamar hukumar Tehran Mustafa Sabetinejad ya bayyana shirye-shiry na karamar hukumar dangane da tattakin Ghadir na tsawon kilomita 10 a birnin Tehran kamar haka: Eid Ghadir yana da sakonni da yawa a gare mu. Yana daga cikin sadaukar da kai a ranar Idin babbar Sallah domin maraba da Idin cikakken ikon addini da tabbatar wilaya da jagorancin al’ummar musulmi bayan wafatin manzon Allah (SAW).
Ya ci gaba da cewa: Karamar Hukumar Tehran ta shirya shirye-shirye daban-daban na al'adu da fasaha na wadannan kwanaki tare da hadin gwiwar tarin kungiyoyi masu ayyukan sa kai da nufin samar da jin dadi da ababen bukata na masu gudanar da tarukan a Tehran.
Yayin da yake ishara da shirin tattaki Eid Ghadir mai tsawon kilomita 10, ya ce: Babban shirin da aka yi a lardin na tsawon lokaci shi ne na babban bikin "Idin Ghadir” wanda zai dauki jama’a a kan titi mai
tsawon kilomita 10." Domin inganta kyakkyawar al'ada da kuma mika wannan koyarwa ga matasa, wani muhimmin bangare na bikin Ghadir mai tsawon kilomita 10 ya shirya liyafa domin mahalarta taron.
Jama’a da kansu ne suke shirya irin wadannan taruka tare da goyon bayan kungiyoyin sa kai, kuma karamar hukuma a shirya take domin taimakawa wajen bayar da gudunmawa a wannan hidima ta jama’a kamar yadda ya kamata.
Zabetnejad ya sanar da yin rajistar sunayen mutane fiye da 2,500 don shiga hidimar wannan taro, ya kuma ce: Manyan masu masaukin baki a wannan gagarumin biki su ne mutanen da kansu, da kuma dimbin kungiyoyin sa kai da suka sadaukar da kansu don halartar wannan taron da bayar da hidima ga jama’a.