IQNA

Bayar da umarnin kotu na karbar daliba da ke sanye da hijabi a makarantar Faransa

23:46 - June 25, 2024
Lambar Labari: 3491407
A bisa wani hukunci da wata kotu a kasar Morocco ta yanke, an umarci wata makarantar Faransa da ke kasar Morocco wadda ta haramta wa wata daliba karatu saboda saka hijabi, da ta mayar da wannan dalib acikin gaggawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na i24news cewa, wata kotu a kasar Morocco ta yanke hukunci kan wata daliba mai lullubi da aka haramtawa shiga wata makarantar Faransa da ke Moroko.

A bisa wannan hukuncin, an tilasta wa wannan makaranta ta Faransa bayar da damar ba wa wannan daliba damar zuwa makaranta sanye da hijabi.

A cewar masu fafutukar kare hakkin bil adama, bayar da wannan hukunci na kotu nasara ce ga daliban da aka haramtawa ‘yancin addini.

Wannan makaranta da ke da alaka da ofishin jakadancin Faransa da ke Maghreb, ta hana dalibar shiga ne saboda hijabinta, wanda ya saba wa dokokin ilimi na Faransa.

Sai dai wata karamar kotu a Maroko ta yanke hukuncin ba ta izinin shiga, yayin da ta ci tarar makarantar Dirhami 5,000 na Moroccan kwatankwacin dalar Amurka 503.

Shafin yada labaran kasar Hespress ya bayar da rahoton cewa, kotun ta yanke hukuncin ne a kan cewa yarjejeniyar hadin gwiwa da raya al'adu tsakanin Morocco da Faransa ba ta kunshi  wani abu na hana sanya tufafin addini ba.

Masu fafutukar kare hakkin bil'adama na Moroko sun yi maraba da wannan hukunci kuma sun dauki matakin a matsayin nasara ta 'yancin fadin albarkacin baki. Adel Chiquito, shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta Moroko ya ce: "Wannan hukunci ya yi adalci ga wannan daliba kuma ana daukarsa a matsayin nasara ga 'yancin ra'ayi da zabi na addini."

 

4223181

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hijabi saka lullubi kotu hukunci addini
captcha