IQNA

Rashin mutunta mata masu lullubi da 'yan sandan Amurka suke yi

15:44 - June 26, 2024
Lambar Labari: 3491411
IQNA - Mujallar "Nation" ta bayyana a cikin wata makala cewa 'yan sandan Amurka sun tilasta wa wasu dalibai mata musulmi cire lullubi yayin da suke murkushe zanga-zangar magoya bayan Falasdinu tare da keta sirrin mata musulmi masu lullubi.

A cewar al-Quds al-Arabi, Mujallar "Nation" ta kasar Amurka ta fitar da wani rahoto da ke cewa 'yan sandan Amurka suna keta hurumin hijabin mata musulmi a fadin Amurka.

Rahoton ya bayyana cewa: Daliban Jami'ar Jihar Ohio sun kaddamar da wani gangamin neman jami'ar ta daina saka hannayen jari a kamfanonin da ke goyon bayan gwamnatin Isra'ila.

 A halin da ake ciki dai, ‘yan sanda sun cafke Samia Hammadmad daya daga cikin daliban wannan jami’a, duk da cewa ba ta a wurin taron masu zanga-zangar, inda suka kai ta gidan yarin Franklin, inda aka bincike ta tare da neman ta cire lullubi na suturar musulunci da ta saka.

Rahoton ya kara da cewa: Duk da bukatar da ta gabatar na a mayar mata da hijabinta, jami’an ‘yan sandan na Amurka sun yi watsi da bukatar, inda ta yi tsawon kwnaki 12 tana tsare ba tare da lullubi a kanta ba.

Wani bangare na wannan rahoto yana cewa: Ba Hammadmad ce kadai aka tauye wa ‘yancinta na addini ba. An dauki da dama daga cikin irin wadannan ayyuka na cin zarafin mata masu lullubi da 'yan sandan Amurka suka yi a yayin da dalibai suke gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu.

Irin wadannan laifukan sun faru ne a jami'o'i daban-daban da suka hada da Jami'ar Jihar Arizona, Columbia, DePaul da kuma Jami'ar Jihar Ohio.

 

4223281

 

 

captcha