IQNA

Sanarwar hadin gwiwa ta 'yan siyasar Amurka 12 da suka yi murabus game da yakin Gaza

16:06 - July 03, 2024
Lambar Labari: 3491450
IQNA - Jami'an gwamnatin Amurka 12 da suka yi murabus saboda matsayin gwamnati kan yakin Gaza, sun yi Allah wadai da manufar Biden kan Gaza, suna masu cewa gazawa ce kuma barazana ce ga tsaron kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arabi 21 cewa, wasu jami’an gwamnatin Amurka 12 da suka yi murabus saboda matsayin gwamnatin Biden dangane da yakin Gaza, sun yi Allah wadai da manufofin Biden kan Gaza a wata sanarwar hadin gwiwa. A cewarsu, wannan manufar ta gaza kuma barazana ce ga tsaron kasa na Amurka.

Goyon bayan da Biden ya yi ba tare da wani sharadi ba ga laifukan da Isra'ila ke yi a Gaza ya sa wasu jami'an gwamnatinsa yin murabus. Sun zarge shi da rufe ido kan laifukan da Isra'ila ke aikatawa a yankin Falasdinu.

Gwamnatin Biden ta musanta hakan, tana mai nuni da sukar mutuwar fararen hula a Gaza da kuma kokarin da take yi na kara kai agajin jin kai a yankin, inda jami'an kiwon lafiya suka ce an kashe mutane kusan 38,000 a hare-haren da Isra'ila ta kai kawo yanzu.

Jami'ai masu barin gado sun bayyana a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a jiya Talata cewa, rikicin da ake ciki ya nuna irin barnar da manufofin Amurka a Gaza ke yiwa Falasdinawa, Isra'ila da kuma tsaron kasar Amurka.

A cikin wannan bayani an ambaci irin goyon bayan diflomasiyya da Amurka ke baiwa Isra'ila da kuma hadin kai da ba za a iya musantawa ba wajen kashe Falasdinawa da yunwa da suke yi wa kawanya a Gaza. Sanarwar ta kuma ce, wadannan manufofin za su yi matukar tauye martabar Amurka a duniya.

 

4224601

 

 

captcha