Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al Furat cewa, ana gudanar da shirye-shiryen tarukar makokin Muharram a Karbala.
A cewar sanarwar Alaa Ziauddin mataimakin babban sakataren hubbaren Imam Husaini (AS) za a gudanar da taron canza tutar kubba ta Imam Husaini (AS) a daren Lahadi mai zuwa 7 ga Yuli, Ana sa ran ranar Litinin ce ta kasance farkon watan Muharram.
Ziauddin ya kuma ce za a gudanar da sauya tutar ne a wani taro na musamman tare da halartar dimbin muminai da kuma kafafen yada labarai.