IQNA

Karrama makarancin kur’ani na kasa da kasa da lakabin Amir al-Qara a hubbaren Abbas

15:26 - July 09, 2024
Lambar Labari: 3491484
IQNA - Hamidreza Ahmadi, mai karatu na kasa da kasa, ya yaba da aikin Amir al-Qurra  na cibiyar kula da harkokin kur’ani mai tsarki ta haramin Abbasi.

Hamidreza Ahmadi, makarancin kur'ani mai tsarki na kasa da kasa, ya halarci hubbaren Abbasi, ya kuma yaba da  shirye-shiryen kur'ani na majalisar kur'ani mai tsarki na wannan wuri mai albarka.

Ahmadi, tare da rakiyar Mohammad Reza Al-Zubaidi, manajan gudanar da ayyukan shirin Amir al-qurra  ya ziyarci cibiyar, inda ya samu bayani dangane da maganganun malaman addini, da suka hada da shugabannin cibiyoyin addini, da jami’an gwamnati, dattijai da kuma malaman kur’ani da suka ziyarci wannan cibiya. .

Ya yi godiya tare da gode wa cibiyar haramin Abbasi da suka kirkiro da kuma tallafawa irin wadannan ayyuka.

A cewarsa, wadannan tsare-tsare za su tada hazikan masu karatu wadanda daga baya za su fafata a matakin kasa da kasa.

Wannan makarancin kur'ani na kasa da kasa ya jaddada cewa: Wannan aiki yana da matukar muhimmanci kuma yana haifar da tarbiyyar kur'ani mai tsarki da samar da abin koyi da kuma samar da  fitattun makaranta na kasa da kasa.

 

4225616

 

 

captcha