Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-kafil cibiyar ilimi da al’adu ta hubbaren Abbasi cewa, bisa shirinta na shekara-shekara na tunawa da abubuwan da suka faru da Ahlul-Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, a wannan shekara, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan watan Muharram, an shirya gudanar da tarukan juyayi ga Aba Abdullah Al-Hussein (AS) a wasu kasashen Afirka.
Shugaban sashen yada labarai na wannan cibiya Sayyid Muslim Al-Jabari ya ce: Ana gudanar da wadannan tarukan ne a kasashe da dama na yankin Bakar fata a cikin watannin Muharram da Safar da nufin yada koyarwar Husaini da kuma bayyana matsayin Husaini. zaluncin da aka yi ma Imam Husaini (a.s.) da iyalansa da sahabbansa.
Ya kara da cewa: Wadannan shirye-shirye sun hada da shirya tarukan zaman makoki da jawabai na musamman na watan Muharram a kasashe irinsu Tanzania, Mauritaniya, Senegal, Ghana, Madagascar, Kenya, Rwanda, Kamaru, Nijar, Najeriya, Jamhuriyar Benin, Saliyo da sauransu.
A Najeriya an gudanar da wannan taro a birnin Kaduna tare da halartar dimbin jama'ar Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su).
Sheikh Ibrahim Musa Yusuf malami mai tablig na sashen ilimi da al'adu na hubbaren Abbasi na wannan birni ya gabatar da jawabi kan falalar kuka dangane da wahalhalun da Imam Husaini (a.s) ya sha a cikin fadin imamai ma'asumai (a.s.).