An Gudanar Da Taruka masu taken Jariran Hussaini Domin Tunawa Da Sayyid Ali Asghar
IQNA – An gudanar da jerin gwano na musamman mai taken taron ‘ya’yan Husaini a Iran da sauran kasashe da dama a ranar Juma’a ta farko ta watan Muharram (12 ga watan Yuli) domin tunawa da jariri Imam Husaini (AS) dan watanni 6 da haihuwa. Sayyidina Ali Asghar (AS), wanda aka kashe shi ba tare da jin kai ba a ranar Ashura a yakin Karbala a shekara ta 680 Miladiyya.