Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, an gudanar da zaman makokin sayyidul shuda’a a jami’ar Musulunci ta Kinshaza karkashin jagorancin majalisar masu hidima ga Ahlul-baiti (AS).
Wannan taro wanda ya samu jawabin Hujjatul Islam wal Muslimin Isma'il Bokasa daga dalibai da 'yan uwa na Jami'atul Mustafa kuma Mugabllig na kasa da kasa, an gudanar da shi ne tsawon kwanaki 11 tare da gudanar da taron al'umma kan maudu'in Harkar Husaini a Jami'ar Musulunci ta babban birnin kasar.