IQNA

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yaba wa bajintar surukar Shahid Isma’il Haniyya

14:25 - August 09, 2024
Lambar Labari: 3491663
IQNA - Bayan shahadar marigayi shugaban ofishin kungiyar Hamas, faifan bidiyo na matar dansa ya yi ta yaduwa a yanar gizo, wanda ya ja hankali dangane da yabon da jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi mata.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yaba wa bajintar surukar Shahid Isma’il Haniyya

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin kula da wallafa ayyukan Ayatullah Sayyid Ali Khamenei cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran cewa, jagoran ya yaba da irin tsayin dakan da wannan iyali ke da shi bayan kallon wannan faifan bidiyo inda ya ce: Ta yi magana mai ma’ana da kuma dacewa, magana mai kyau da sosai."

A cikin wannan faifan bidiyo da aka nada a Gaza, surukar shahid Haniyyah ta ce: “A cikin zuciyata ta gamsu da kaddarar Ubangiji, ina shelanta shahadar wani mutum da sama da kasa ke tunawa da shi sosai; Mutumin da sadaukarwarsa ba ta misaltuwa.

Ya shiga cikin mujahidai, masu gaskiya masu albarka, da ‘ya’yansa shahidai da dukkan wadannan tsarkakakkun jinanansu.

Ya kasance jarumi, kwamanda kuma babban shahidi. Sai dai mu fadi abinda Allah ya yarda kuma ya kaddara kuma mu karbi hakan.

Ya Allah ka saka mana a cikin bala'in da muke ciki, kuma ka kyautata makwancinmu.

Wannan babban bala'i ne, amma abin da ke sanyaya zuciyarmu shi ne, duniyar nan mai karewa ce kuma za mu hadu a cikin aljanna mai fadi kamar sama da kasa da yardarm Allah.

 

 

 
 

 

captcha