Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wata mace ‘yar asalin kasar Ireland wadda kuma Kirista ce mai suna “Tara O’Grady” ta yi fama da cutar kansa na wani lokaci kuma ta warke daga wannan cuta bayan da kai koken wajen Imam Hussain (AS) a lokacin Arbaeen. Don haka ta yanke shawarar shiga tattaki daga Najaf zuwa Karbala.