Shafin yada labarai na Al-Furat ya bayar da rahoton cewa, maziyarta daga kasar Iraki da kuma kasashen duniya daban-daban sun gudanar da zaman makoki dangane da zagayowar ranar wafatin manzon Allah (S.A.W) a hubbaren Alawi da ke Najaf Ashraf.
A game da haka, gwamnatin Najaf Ashraf, tare da hadin gwiwar hubbaren Alawi, sun aiwatar da shirin tsaro, hidima da kiwon lafiya, na karbar masu ziyara.
Ma'aikatan tsaro da na Hashd al-Shaabi (Popular Mobilisation) sun shiga cikin wannan shiri na tsaro, kuma sun mayar da hankali ne kan kokarin leken asiri da ayyukan tabbatar da tsaron lardin Najaf da yankunan da ke kewaye da shi da kuma hanyoyin da za su kai ga Garin Najaf, da isar masu ziyara zuwa haramin Amirul Muminin (a.s).