IQNA

An kammala gasar kur'ani mai tsarki ta Afirka karo na 5 a Morocco

16:50 - September 30, 2024
Lambar Labari: 3491957
IQNA - A jiya 29 ga watan Satumba a birnin Fez na kasar Moroko aka kammala gasar haddar kur'ani mai tsarki karo na 5 na mu'assasar malaman Afirka ta Muhammad VI.

Shafin ar.hibapress.com ya habarta cewa, a ranar 26 ga watan Satumba ne aka fara gudanar da jarabawar karshe na wannan gasa a birnin Fez kuma an ci gaba da yin gwajin har tsawon kwanaki uku.

Reshen gidauniyar Muhammad VI a kasashen Afirka 48 ne suka halarci wadannan gasa kuma mutane 118 wadanda 12 daga cikinsu mata ne suka fafata a wadannan gasa ta yanar gizo da kuma nesa.

Kwamitin alkalan gasar na wannan gasa ya hada da alkalan kasar Maroko da wasu kasashen Afirka wadanda suka tantance gasar da wadanda suka halarci gasar ta Fez.

Har yanzu ba a bayyana sunayen wadanda suka yi nasara a gasar ba a kafafen yada labarai a hukumance; Sai dai a wajen rufe gasar da kuma na karshe, jami’an gasar sun gabatar da wadanda suka fi nuna kwazo a kowane fanni tare da karrama su.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4239781

 

captcha