Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Kafofin yada labaran gwamnatin haramtacciyar Kasar Isra'ila suna bayar da rahotanni kan ruwan makamai masu linzami da Iran ke yi a kan yankunan da aka mamaye da kuma kunna karaurawar gargadi a dukkan yankunan Falastinu da Isra'ila ta mamaye.
Wasu majiyoyi sun sanar da cewa an harba rokoki akalla 102 daga Iran zuwa yankunan da aka mamaye.
An yi ta jin karar faɗakarwa a manyan yankunan da aka mamaye, ciki har da Quds da aka mamaye, da Biyersheba da kewayen hamadar Negev.
Ma'aikatar harkokin wajen yahudawan sahyoniya ta sanar da cewa daukacin matsugunan yahudawan sahyoniya sun tsere zuwa wuraren boya na karkashin kasa.
Kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun bayar da rahoton cewa, wasu makaman roka sun afkawa "Tel Aviv" da birnin Kudus da aka mamaye da kuma yankunan kudancin yankunan da aka mamaye.
Wasu kafafen yada labarai sun ruwaito adadin makaman da aka harba daga Iran a matsayin makamai masu linzami 400.
Yediot Aharonot ya sanar da cewa an kai hari kan wani gini da ke arewacin Tel Aviv.
Kazalika, wasu kafafen yada labarai sun bayar da rahoton cewa rokoki sun afkawa wasu wurare da dama a yankunan da aka mamaye.
Kazalika, kafofin yada labaran gwamnatin Sahayoniya sun sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin sama na "Ben Gurion" da ke birnin Tel Aviv.
Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewa a shirye Amurka take ta taimakawa gwamnatin sahyoniyawan domin abin da ya kira "kare kanta daga hare-hare da kuma tallafawa dakarunta a yankin".
Kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun bayar da rahoton cewa, wasu makaman roka sun afkawa "Tel Aviv" da birnin Kudus da aka mamaye da kuma yankunan kudancin yankunan da aka mamaye.
Wasu kafafen yada labarai sun ruwaito adadin makaman da aka harba daga Iran a matsayin makamai masu linzami 400.
Kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun sanar da hare-haren makamai masu linzami na Iran karo na biyu a kan yankunan da aka mamaye.
Gidan rediyon sojojin yahudawan sahyoniya ya sanar da cewa: Lamarin bai kare ba kuma mai yiyuwa ne a samu wasu hare-haren makamai masu linzami daga Iran.
Wasu kafafen yada labaran yahudawan sahyoniya sun kuma bayyana harba makaman da kasar Iran ke yi kan yankunan da aka mamaye da cewa ba ta tsaya ba.
Tashar talabijin ta 14 ta gidan talabijin na gwamnatin Sahayoniya ta kuma sanar da cewa dukkanin yahudawan sahyoniya sun tsere zuwa matsugunan.
Jaridar New York Times ta sanar da cewa: Da alama makaman roka na Iran sun isa Isra'ila cikin kasa da mintuna 15. Wannan yana nufin cewa wadannan makamai masu linzami na ballistic ne.
Jaridar New York Times ta sanar da cewa: Da alama makaman roka na Iran sun isa Isra'ila cikin kasa da mintuna 15. Wannan yana nufin cewa wadannan makamai masu linzami na ballistic ne.