Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto shugaban mabiya darikar katolika na duniya ya mayar da martani dangane da ci gaba da aikata laifukan gwamnatin sahyoniyawan a kasar Labanon.
A jiya Asabar fadar Vatican ta nakalto Paparoma Francis shugaban mabiya darikar Katolika na duniya yana cewa Paparoma yana goyon bayan samar da zaman lafiya a yammacin Asiya.
A cewar Fafaroma Francis, fadar Vatican ba za ta iya yin shiru ba dangane da irin wahalhalun da bil'adama ke fuskanta a Lebanon.
A makon da ya gabata ne shugaban mabiya darikar Katolika na duniya ya yi kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a kasashen Lebanon, Gaza da sauran yankunan Falasdinu da ke mamaye da su, a daidai lokacin da gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da kai hare-hare kan kasar Labanon.
A karshen ziyararsa a Belgium Paparoma Francis ya ce: Ina rokon dukkanin bangarorin da su gaggauta tsagaita wuta a kasar Lebanon, Gaza da sauran Falasdinu.
Jagoran mabiya darikar Katolika na duniya ya kara da cewa: Labanon sako ne, amma a halin da ake ciki yanzu sako ne da ake tarwatsa shi. Wannan yakin ya yi babbar illa ga mutane; Mutane da yawa suna mutuwa kowace rana a Gabas ta Tsakiya.