A cewar shafin Arabic 21, zaɓen Amurka na 2024 yana wakiltar wani muhimmin lokaci ga kungiyoyin jama'a da yawa, kuma masu jefa ƙuri'a na musulmi suna da yanayi mai sarƙaƙiya a tsakaninsu.
A cewar rahoton, Musulmai masu jefa kuri'a bisa ga al'ada sun karkata ga jam'iyyar Democrat, galibi suna yin la'akari da dabi'u guda daya game da adalci na zamantakewa, 'yancin jama'a da sake fasalin shige da fice. Sai dai abubuwan da suka faru a baya-bayan nan - musamman tashe-tashen hankula a Gaza - sun haifar da gagarumin sauyi a halayensu. Ta yadda yakin zirin Gaza ya kasance wani muhimmin al'amari na rarrabuwar kawuna tsakanin musulmi masu jefa kuri'a, kuma martanin gwamnatin Biden kan wannan rikici ya sha suka daga al'ummar musulmi. Da dama dai na ganin cewa taimakon da Amurka ta baiwa Isra'ila na soji ya taimaka wajen cin zarafin Falasdinawa, kuma Biden bai cika yin Allah wadai da matakin na Isra'ila ba.
Kuri'un na baya-bayan nan sun nuna an samu gagarumin sauyi na goyon bayan masu kada kuri'a na musulmi a zaben 2024. Bisa kididdigar kuri'ar jin ra'ayin jama'a na Majalisar Dangantakar Musulunci ta Amurka (CAIR) da aka gudanar a ranakun 30 da 31 ga watan Oktoban 2024, kashi 41 cikin 100 na masu jefa kuri'a musulmi ne kawai ke shirin marawa 'yar takarar Democrat Kamla Harris baya. Wannan shi ne yayin da kashi 42 cikin dari suka bayyana goyon bayansu ga Jill Stein, 'yar takarar jam'iyyar Green Party. Hakan dai na nuni da raguwar goyon bayan musulmi ga 'yan takarar jam'iyyar Democrat, wanda ya kasance tsakanin kashi 80 zuwa 92 cikin dari a zaben da ya gabata.
A daya hannun kuma, rashin amincewa da dan takarar jam'iyyar Republican (Donald Trump) da musulmi masu kada kuri'a suka yi, na nuni da cewa sun fice daga 'yan takarar manyan jam'iyyun biyu, suna komawa ga 'yan takara masu kusanci da kimarsu.