IQNA - An buga wani faifan bidiyo na wani yaro Bafalasdine yana rera kiran sallah a kan tankin ruwa na sansanin Falasdinawa na Gaza a yanar gizo.
A rahoton tashar Aljazeera, wannan yaro Bafalasdine ya haura daga tankar ruwan da ke sansanin ‘yan gudun hijira a Gaza inda ya yi kiran sallah bayan ruguza masallatai a zirin Gaza da gwamnatin sahyoniya ta yi.