A cewar Anatoly, daruruwan mutane a Stockholm babban birnin kasar Sweden sun soke bikin sabuwar shekara domin nuna goyon baya ga al'ummar Gaza da Falasdinu tare da gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayansu.
Jiya da yamma, Talata, domin amsa kiran da dama daga kungiyoyi masu zaman kansu na kasar, masu zanga-zangar sun taru a dandalin birnin duk da sanyin da ake ciki.
A maimakon bikin sabuwar shekara, masu zanga-zangar sun bayyana bakin cikin su ga kananan yara da fararen hular Palasdinawa da Isra'ila ta kashe a yakin kisan kare dangi da aka fara a ranar 7 ga Oktoba, 2023 kan Gaza.
Masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa majalisar dokokin kasar Sweden tare da dauke da tutoci masu rubuta "Yancin Falasdinu, 'Yancin Gaza", "Dakatar da kisan kiyashi" da "Kauracewa Isra'ila".
Magoya bayan Falasdinu a kasar Sweden sun yi kira da a kawo karshen kisan kiyashin da haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a Gaza cikin gaggawa, suna rera taken "'yanci ga Falasdinu," "Dakatar da mamaya" da "Isra'ila mai kisa."
Dangane da goyon bayan da kasashen Sweden da Amurka suke baiwa Isra'ila, masu zanga-zangar sun sanar da cewa, wadannan kasashe biyu na da hannu wajen aikata laifukan yaki na Tel Aviv.
Wata sanarwa da aka karanta a madadin masu zanga-zangar ta ce ba sa bikin sabuwar shekara ne saboda kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa yara, mata da ‘yan jarida.