IQNA

Sakatare Janar na Nojaba ya yaba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci a lokacin guguwar Al-Aqsa

14:57 - February 09, 2025
Lambar Labari: 3492711
IQNA - Sheikh Akram Al-Kaabi, wanda ya yaba da goyon baya da jagorancin Ayatullah Khamenei, ya kira tsarin tsayin daka a matsayin wanda ya yi nasara a yakin Al-Aqsa, sannan ya ba da tabbacin cewa a nan gaba kasar Siriya da sauran yankuna za su shiga cikin wannan akidar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar yada labaran Harkar Nujaba ta bayyana cewa, babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Nujaba ta kasar Iraki a cikin wani sakon bidiyo da ya fitar, ya taya dukkanin 'yantattun al'ummar duniya musamman bangaren juriya karkashin jagorancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga Gaza da Labanon zuwa kasashen Yaman da Iraki dangane da nasarar da Palastinawa suka samu a yakin guguwar Aqsa, tare da mika sakon gaisuwa ga dukkanin mayaka.

Sheikh Akram Al-Kaabi ya bayyana cewa, mun dakatar da ayyukanmu ne bayan tsagaita bude wuta a Gaza, amma idan makiya suka dawo fagen daga, za mu koma fagen daga, ya kuma kara da cewa: Ba za mu taba yin watsi da al'amarin da ya fi muhimmanci a duniyar Musulunci ba, wato Al-Quds Al-Sharif.

Yayin da yake nuna godiya ga jajircewar jagorancin Imam Khamenei da goyon bayan dakarun kare juyin, ya ci gaba da cewa: Ya dace a rika tunawa da manyan shahidan gwagwarmaya Sayyed Hassan Nasrallah, Ismail Haniyyah, Yahya Sinwar, da shahidan Iraki na tafarkin Qudus, Abu Taqi da Abu Baqir, da kuma nuna godiya ga kabilar Iraki.

Yayin da yake tunawa da cewa karfin daular tsayin daka yana fitowa ne daga ikon Allah Madaukakin Sarki kuma yana kara karuwa, Al-Kaabi ya jaddada cewa: “Muna dogara ne da hadin kai da kuma kara karfin daular mu, kuma ba mu da bukatar Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar kasashen Larabawa da makamantansu.

Akram Al-Kaabi ya bayyana kisan kiyashin da aka yi a Gaza da kuma laifin fashewar pager a kasar Labanon a matsayin Holocast na gaske kuma mafi muni fiye da laifuffukan kungiyar ISIS, ya kuma ce: Turawa ma manyan abokanan Isra'ila ne kan wadannan laifuka, saboda sun zaunar da sahyoniyawa a Palastinu, kuma suna goyon bayansu.

Daga nan sai ya bayyana abubuwan da ke faruwa a kasar Sham yana mai cewa: “Masu ganin cewa turbar juriya ta yi hasarar kasar Siriya, to su dan dakata su ga cewa, in Allah ya yarda, kasashen Siriya da sauran yankuna za su shiga cikin tsarin tsayin daka.

Ya kira masu goyon bayan kasancewar Amurka a kasar Iraqi maciya amana, ya kuma ce wa sojojin haya na Washington: "Kuna tsoron Trump wawa, amma ba mu da tsoronsa saboda ba ma tsoron mutuwa." Takalmin mafi kankantar mujahidan Iraqi ya fi Trump da ire-irensa daraja.

 

 

4264889

 

 

captcha