Shugaban jam'iyyar StramKurs mai tsatsauran ra'ayi Rasmus Paludan, wanda ya sha kona kur'ani a kasashen Sweden da Denmark, ya gabatar da wata sabuwar bukatar kona kur'ani mai tsarki, amma hukumomin Denmark sun yi watsi da wannan bukata tare da haramta masa kona kur'ani a babban birnin kasar.
Rasmus Paludan ya yi ikirarin cewa hukumomin Denmark sun hana shi 'yancin fadin albarkacin baki; Daga baya ‘yan sandan Copenhagen sun tabbatar da cewa an ki amincewa da bukatar Rasmus Paludan kuma an hana shi shiga duk wata zanga-zanga. Da yake tabbatar da hukuncin nasu, 'yan sandan Denmark sun ce: "Bisa wani takamaiman tantancewa, 'yan sanda sun ba da umarnin hana Rasmus Paludan shiga zanga-zangar da ke tsakanin iyakokin 'yan sanda."
Rasmus Paludan, wanda ke da uba dan kasar Sweden, da kuma mahaifiyarsa ‘yar kasar Denmark, a shekarun baya-bayan nan ya shahara wajen kona kwafin kur’ani a kasashen Sweden da Denmark. Ya yi iƙirarin cewa bai damu da lafiyarsa ba saboda yana zaune a Denmark, ba Sweden ba.
A makon da ya gabata ne Paludan ya yi ikirarin cewa kafar sada zumunta ta X ta toshe asusunsa saboda ya rika wallafa abubuwan da suka saba wa Musulunci da kuma daukaka Silwan Momi.
Ya ce an dakatar da asusunsa har sai ya amince da bukatar X na cire bidiyon guda hudu. Hotunan bidiyon sun hada da fitowar sa a gaban ofisoshin jakadancin Turkiyya da Pakistan da kuma Indonesiya, inda ya gabatar da wani jawabi da ya saba wa addinin Musulunci da hotuna na kona kur’ani.