Kamar yadda kafar yada labarai ta Al-kafeel ta ruwaito, shirin farko na wannan shiri da ake watsawa a kafar sadarwa ta Waha Al-Riyahin mai alaka da bangaren Fatima Bint Asad (AS) ya fara ne a daidai lokacin da aka haifi Sayyiduna Abu al-Fadl al-Abbas (AS).
Shirin Siraj Al-Riyahin yana da bangarori da dama da suka hada da hikayoyi, darussa, da gyare-gyare kan karatun suratul Fatiha, wanda yara suka yi marhabin da su.
Ana watsa wannan shiri a duk safiyar ranar Asabar da karfe 11:00 na safe a tashar Waha Al-Riyahin.