Shafin Global Kafeel Network ya bayar da rahoton cewa, Mushtaq al-Ali shugaban majalisar ilimin kur'ani mai alaka da hubbaren Abbas.
Ya kara da cewa: Jami'ai da dama daga ma'aikatar kula da al'adu ta kasar Iran da hukumar kula da al'adu da sadarwa ta Musulunci, da kuma dimbin jami'ai daga rumfuna da suka halarci wannan baje koli da maziyartan wannan taron kur'ani, sun halarci bikin.
Cibiyar ilimin kur'ani ta Astan Abbasi ta halarci bikin baje kolin kur'ani na kasa da kasa karo na 32 a nan Tehran da nufin yada al'adun kur'ani mai tsarki a tsakanin kungiyoyi daban-daban a cikin al'umma, da karfafa wayar da kan addini, da kiyaye dabi'un Musulunci.
A ranar Laraba 5 ga watan Maris ne aka fara bikin baje kolin kur'ani na kasa da kasa karo na 32 a birnin Tehran mai taken "Alkur'ani, tafarkin rayuwa" a dakin taron Imam Khumaini (RA) wanda kuma zai ci gaba har zuwa Lahadi 16 ga watan Maris. Bangaren kasa da kasa na wannan baje kolin, kasashe irin su Iraki, Pakistan, Turkiyya, Rasha, Aljeriya, Bosnia da Herzegovina, Ivory Coast da dai sauransu sun hallara, kuma masu fasaha daga wadannan kasashe sun baje kolin ayyukan kur'ani da zane-zane ga jama'a.