A cewar sashin hulda da jama'a da yada labarai na kungiyar al'adun muslunci da sadarwa, gudanar da wannan taro na kur'ani ya samo asali ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin hukumar kula da harkokin al'adu ta kasar Iran a kasar Indonesia, da masallacin Al-Amjad na lardin Banten, da birnin Tangerang, da masallacin Al-Amjad, da kuma cibiyoyin kur'ani na cikin gida. Wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron sun yi kira ga dukkanin cibiyoyin kur’ani da su karfafa rawar da kur’ani ke takawa a cikin zamantakewar al’ummar musulmi ta hanyar fadada shirye-shiryen ilimantarwa da ingantawa.
A farkon wannan biki, jakadan kur’ani na kasar Iran Hamed Shakernejad ya bayyana muhimmancin karatun kur’ani da hardar kur’ani a cikin al’ummar musulmi, ya kuma bayyana ayyukan Indonesiya a wannan fanni a matsayin abin koyi.
Makarancin na kasa da kasa ya kuma bukaci mahalarta taron da su karfafa alakarsu da kur’ani ta hanyar amfani da yanayi na ibada na watan Ramadan.
Ya kuma jaddada wajibcin gudanar da bukukuwan watan Ramadan daga dukkan bangarori na al'umma, ya kuma bayyana cewa: Diflomasiyyar kur'ani mai tsarki musamman a kasashen musulmi kamar Iran da Indonesiya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tausayawa da kuma kusantar da zukata tsakanin al'ummomi.
Muhimmin rawar da kungiyar al'adu ke takawa wajen bunkasa mu'amalar kur'ani ta kasa da kasa
Shakernejad ya kara da cewa: Kungiyar Al'adun Sadarwa ta Musulunci ta dauki kwararan matakai kan wannan al'amari tare da shirye-shirye kamar da'irar kur'ani ta hadin gwiwa a kasar Indonesia.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da kokarin da makiya suke yi na haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmin duniya, jakadan kur'ani na kasarmu ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kodayaushe ta kasance mai kiyaye hadin kan kasashen musulmi, kuma tana raya dangantakarta da dukkan kasashe bisa mutunta juna da hadin gwiwa a fannin al'adu da addini.