A jajibirin ranar 19 ga watan Ramadan, wanda kuma shi ne daren shahadar Imam Ali (AS), a haraminsa mai alfarma ana shirye-shiryen makoki, inda aka bakaken tutoci da kyallaye, sannan kuma ma'aikatan hubbaren suna tarbar masu ziyara da makoki, rike da bakaken tutoci.
Don haka a jajibirin ranar shahadar Imam Ali (AS) an lullube wurin da bakaken kyallaye, sannan aka daga tutar zaman makoki a saman barandar haraminsa da ke Najaf a daren farko na daren lailatul kadari.