A daidai lokacin da ake gudanar da azumin watan Ramadan, cibiyar binciken kur'ani ta Tebyan ta shirya baje kolin kur'ani na musamman a birnin Srinagar.
An fara wannan taron ne a ranar 23 ga watan Ramadan kuma ana ci gaba da gudanar da shi har tsawon kwanaki uku.
An baje kolin ayyukan fitattun mawallafin rubutu a wurin baje kolin na Srinagar, kuma masu sha'awar fasahar muslunci da kur'ani sun kai ziyara.
A kasa ga hotuna daga baje kolin, Obaid Mukhtar: