IQNA

Mai magana da yawun kungiyar Hamas ya yi shahada a wani harin Isra'ila a Gaza

14:42 - March 27, 2025
Lambar Labari: 3492995
IQNA - Majiyar cikin gida ta bayar da rahoton shahadar Abdel Latif al-Qanua kakakin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas a harin da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta kai kan birnin Jabalia da ke arewacin zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya bayar da rahoton cewa, cibiyar sadarwa ta Al-Aqsa da ke da alaka da kungiyar Hamas ta sanar da cewa: Abdul Latif Qanun ya yi shahada a safiyar yau alhamis, a wani hari da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a kan tantinsa da ke yankin Jabalia da ke arewacin zirin Gaza.

Dangane da haka kungiyar Hamas ta kuma sanar da shahadar Al-Qanua a cikin wata sanarwa da ta fitar tare da jaddada cewa: Jinin shahidai amana ce da ba za ta taba bata ba, kuma ba za mu taba yin sulhu da 'yan mamaya ba. 

A daren jiya ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta tsananta kai hare-hare kan gidajen 'yan gudun hijirar Palasdinawa da tantuna a yankuna daban-daban na zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadin shahadar Palasdinawa da dama.

A cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kashe Falasdinawa 830 tare da jikkata wasu 1,787 wadanda yawancinsu yara da mata ne, tun bayan barkewar kisan kiyashi a Gaza a ranar 18 ga watan Maris. Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa, Falasdinawa kusan 124,000 ne suka sake barin matsugunansu bayan sake kai hare-hare a zirin Gaza da kuma bayar da umarnin ficewa daga Isra'ila.

 

 

4273838

 

 

captcha