IQNA

Shahadar wani kusa a kungiyar Hamas bayan harin da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon

19:18 - April 04, 2025
Lambar Labari: 3493040
IQNA - An kashe shugaban Hamas Hassan Farhat, wanda aka fi sani da Abu Yasser, da wasu mutane biyu a wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai a wani gida a birnin Sidon, dake kudancin kasar Lebanon, a safiyar yau Juma'a.

A cewar Al-Mayadeen, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai wani hari ta sama kan wani gida da ke birnin Sidon da ke kudancin kasar Lebanon, inda ya kashe shugaban Hamas Hassan Farhat da wasu mutane biyu.

A cewar rahoton, sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun kai hari a Al-Naqoura, Nabatiyeh, da Sidon a kudancin kasar Lebanon a yammacin ranar Alhamis, inda suka yi barna a yankunan da aka kai harin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na "Russia Today" ya bayar da labarin cewa: Bisa kididdigar farko da aka yi, "Hassan Farhat, wanda aka fi sani da Abu Yasser", shugaban kungiyar Hamas, da dansa da 'yarsa sun yi shahada a wani hari da jiragen Isra'ila suka kai a wani gida a yankin Dala'a a tsakiyar Sidon. A wannan harin da aka kai ta hanyar amfani da jirgi maras matuki, an harba makamai masu linzami guda biyu a gidan.

Kawo yanzu kungiyar Hamas ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da shahadar Farhat ba, amma an rika yada hotunan gidan da aka kai hari tare da cire gawar Farhat a shafukan sada zumunta.

A safiyar jiya (Alhamis) jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hari kan garin Al-Naqoura da ke yammacin kudancin kasar Lebanon a lokuta da dama.

Dangane da haka ne ma'aikatar lafiya ta kasar Labanon ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa akalla mutane uku ne suka mutu kana wasu biyu kuma suka jikkata sakamakon wani hari da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan wani gida da ke birnin Sidon da wata mota da ke kan titin Bint Jbeil da ke kudancin kasar Lebanon a safiyar yau Juma'a.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta kasar Labanon ta fitar, ta yi Allah wadai da harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan motocin daukar marasa lafiya guda biyu da wata motar kashe gobara, da kuma lalata cibiyar kula da lafiya ta wucin gadi ta hukumar lafiya a garin Al-Naqoura da ke kudancin kasar, tare da yin kira ga kasashen duniya da kada su kyale ko kuma su yi watsi da wadannan hare-hare masu hadari, wadanda ke nuna karara karya dokokin kasa da kasa da ka'idojin kungiyoyin agaji.

 

4274685

 

 

 

 

captcha