Kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait ya habarta cewa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi, Hussein Ibrahim Taha, ya mika ta'aziyya ga shugaban fadar Vatican bisa rasuwar Paparoma Francis a wata sanarwa da ya fitar. Ya yaba da matsayin Paparoma Francis na jin kai da kuma rawar da ya taka wajen inganta tattaunawa tsakanin addinai da kuma kare mafiya rauni a cikin al'ummomi.
Ya jaddada cewa mutuwar Paparoma Francis babban rashi ne ga duniya, domin ya kasance mai fafutukar kare hakkin bil adama da ka'idojin hakuri da zaman tare. Matsayinsa na jajircewa wajen samar da zaman lafiya da adawarsa da cin zarafi da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa, musamman a zirin Gaza, sun yi fice kuma suna da kyau.
Fadar Vatican ta sanar a ranar Litinin 1 ga watan Mayu cewa Paparoma Francis shugaban mabiya darikar Katolika na duniya wanda ya dade yana fama da rashin lafiya ya rasu yana da shekaru 88 a duniya.
Paparoma Francis, Bishop na Roma kuma shugaban cocin Katolika, ya zama Paparoma a shekara ta 2013 bayan murabus din Benedict na 16. Shi ne Paparoma na farko daga Amurka, memba na farko na tsarin Jesuit, kuma Paparoma na farko wanda ba na Turai ba tun Paparoma Gregory III a karni na 8.
A lokacin sarautar Paparoma Francis ya sha tallafawa wadanda ke fama da yaki da yunwa da kuma wadanda ke fama da talauci, lamarin da ya sa wasu ke kiransa da "Papapaan Jama'a."
Paparoma ya sha yin kira da a kawo karshen yakin Gaza da kuma kawo karshen laifukan da yahudawan sahyuniya suke yi kan al'ummar Palastinu. A ranar Lahadin da ta gabata, ya halarci bikin Easter a St. Peter's Basilica a cikin Vatican a cikin keken guragu sannan ya gabatar da jawabi ga dimbin mabiya da maziyarta a harabar cocin.
Wasu gungun mutane da ‘yan siyasa daga kasashen musulmi sun aike da sakon ta’aziyyar rasuwarsa.