IQNA

Jakadiyar Kasar Finland da Hijabi a Haramin Imam Husaini (AS)

16:32 - April 29, 2025
Lambar Labari: 3493172
IQNA - Anno Saarila Jakadiyar Finland a kasar Iraki ta yi bayani kan irin yadda ta samu sanye da hijabi a  Iraki  a lokacin da ta halarci hubbaren Imam Husaini (AS).

A yayin wannan ziyara, Anu Sarila ta ziyarci hubbaren Imam Husaini (AS) inda ta samu labarin ayyuka daban-daban na wannan wuri da kuma shi kansa Imam Husaini, ta kuma yaba da ayyuka daban-daban da wannan harami ke yi ga masu ziyara.

Haka nan kuma yayin da take ishara da ziyarar da ta yi a hubbaren Imam Husaini (AS) da ke Karbala, ta ce: Hakika wannan ziyara ta yi kyau, kuma haramin Husaini ya kasance wuri mai ban sha'awa.

Jakadiar kasar Finland a Iraki ta kuma yi magana game da yadda ta samu damar sanya hijabi irin na kasar Iraki inda ta ce: Abokin aikina ya taimake ni da wannan. "Na taba zuwa Najaf a baya, don haka na samu gogewar amfani da abaya."

Annu Saariella, jakadiyar Finland a Iraki, ta yi aiki tun 2023.

 

 

 
 
 

 

 

captcha