A cikin sakon da ya fitar a wannan Alhamis 26 ga watan Yuni 2025, Jagoran ya ce Iran ta murkushe gwamnatin Isra'ila tare da durkusar da ita kan gwiwarta, da nuna wa Washington cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran na iya isa sansanonin Amurka masu muhimmanci a yankin tare da daukar matakan yaki da su.
Ga matanin sakon kamar haka:
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai
Sallama da a gaisuwa ga al'ummar Iran.
Na farko ina girmama shahidai masu daraja da suka hada da shahidai kwamandoji da masana kimiyya wadanda suke da kima ga Jamhuriyar Musulunci da kuma yi mata hidima a cikin aminci. A yau suna samun ladan hidimar da suka yi a wajen Allah madaukakin sarki.
Ina ganin ya zama dole in taya al'ummar Iran murna. Ina taya su murna a kan abubuwa kamar haka:
Da farko ina taya murna ga nasara akan gwamnatin sahyoniyawa.
Gwamnatin yahudawan sahyoniya tare da duk surutu da alfaharinta, an murkushe su tare da durkusar da ita. Tunanin cewa irin wadannan hare-hare na martini mai karfi zai iya fitowa daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba shiga zukatansu ba, amma hakan ya faru.
Mun gode wa Allah da Ya taimaka wa Sojojinmu, Ya ba su damar kutsawa cikin ci gaban da suke da shi, a bangaren tsarin tsaro, da kuma nasara samun wurare da ake bukatar kaiwa hari a cikin yankunansu na birane da na soji, da harba makamai masu linzami da wasu makaman na zamani.
Wannan yana daga cikin mafi girman ni'imomin Allah. Yana tabbatar da cewa dole ne gwamnatin Sahayoniya ta fahimci cewa wuce gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran abu ne mai tsadar gaske, mai matukar wahalar jure masa.
Cikin ikon Allah ne hakan ta faru, kuma tabbas Sojojin mu da al’ummar mu sun cancanci yabo, wadanda su ne suka tallafa wa wadannan rundunonin, suka karfafa su don cimma wannan gagarumar nasara.
Taya murna ta biyu ga nasarar da Iran ta samu kan gwamnatin Amurka.
Gwamnatin Amurka ta shiga cikin fada kai tsaye domin ta fahimci cewa idan ba ta shiga ba, za a shafe gwamnatin sahyoniyawan gaba daya. Sun shiga ne don ceto gwamnatin yahudawa, amma ba su sami komai daga wannan yakin ba.
Sun kai hari kan cibiyoyin mu na nukiliya, wadda take gudana a bisa doka ta duniya, duk da haka ba su cimma wani muhimmin abu ba. Shugaban na Amurka ya sake yin karin gishiri a cikin bayanin abin da ya faru a fili, a wannan wuce gona da iri.
Duk wanda ya saurara zai iya fahimtar cewa a cikin kalamansa akwai tufka da warwara, kuma za a fahimci cewa: sun gaza a kan cimma manufofinsu, kuma sun yi aikin wuce gona da iri don boye gazawarsu. A nan ma Jamhuriyar Musulunci ta samu nasara, inda ta mayar da kakkausan martani a kan fuskar Amurka, ta hanyar kai hari kan daya daga cikin muhimman sansanonin sojin Amurka yankin, tare da yin barna.
Wadanda suka wuce gona da iri a halin yanzu suna kokarin su kawar da hankulan duniya, suna da'awar "babu abin da ya faru", lokacin da a zahiri wani babban lamari ne ya faru. Kasancewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana iya kaiwa ga muhimman sansanonin Amurka a yankin da kuma aiwatar da aikin farmaki na martani wannan ba karamin lamari ba ne, kuma za a iya maimaita hakan a nan gaba. Duk wata arangama a nan gaba za ta kasance mai tsada ga abokan gaba.
Na uku taya murna ga hadin kan al'ummar Iran.
Cikin ikon Allah, al’ummar da ke da kusan mutane miliyan 90 ta tsaya a dunkule, kafada da kafada, ba tare da rarrabuwar kawuna a cikin bukatu ko manufa ba. Sun daga murya, suna rera take, tofa albarkacin bakinsu, tare da goyon bayan ayyukan da Sojoji ke yi, kuma hakan zai ci gaba.
Al'ummar Iran sun nuna matsayinsu da sanannun halayensu, tare da tabbatar da cewa a lokacin larura wannan al'umma tana magana da murya daya. Kuma da yardar Allah hakan ta kasance.
Wani muhimmin batu da nake son jaddadawa shi ne, kwanan nan shugaban Amurka ya ce dole ne Iran ta mika wuya. Mika wuya! Wannan ba batun bunkasa ayyukan cibiyoyin nukiliya ba ne, Tabbas irin wadannan kalaman sun tabbar da cewa manufar shelanta yakin ita ce sanya Iran ta mika wuya.
Iran mai girma, mai tarihi, al'adu, da tunani na sadaukarwa da kare kasa, wani ya yi tunanin mika wuya ga irin wannan kasa abin dariya ne ga wadanda suka san al'ummar Iran.
Amma bayanin nasa ya bayyana gaskiya: Tun daga farkon juyin juya halin Musulunci, Amurka ta kasance tana rikici da Iran mai bin tsari da manufa ta Musulunci, inda a kullum take neman sabbin uzurori, irin su 'yancin dan Adam, dimokuradiyya, 'yancin mata, batun nukiliya, ci gaban makamai masu linzami, amma babban batu abu daya ne, shi ne Iran ta mika wuya kawai.
Shugabannin Amurka da suka gabata ba su fadi hakan ba kai tsaye saboda ba za a yarda da su ba, babu wata doka da ta yarda da gaya wa wata al'umma, "Ku zo, mika wuya". Don haka suka boye wannan manufa. Amma wannan mutumin ya fallasa gaskiyar lamarin: Amurka ba za ta amince da komai ba face Iran ta mika wuya. Wannan batu ne mai mahimmanci! Wajibi ne al'ummar Iran su san cewa wannan shi ne tushen rikici da Amurka, wannan furuci babban cin fuska ne ga Iran, kuma wannan ba zai taba faruwa ba.
Iran kasa ce mai karfi da fadi wacce take da dadadden tarihi da al’adu wanda ya fi na Amurka da makamantanta. Tsammanin cewa Iran za ta mika wuya ga wata kasa, rudu ne da ba za a taba mantawa da shi ba, wanda zai shiga cikin kwandon tarihi na masu hankali da ilimi.
Al'ummar Iran sun yi nasara kuma za su ci gaba da kasancewa a haka da yardar Allah. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya kiyaye wannan al'umma a karkashin ni'imarsa da daraja da daukaka, ya daukaka darajar Imam (Khumaini), kuma ya ba wa Imam Mahdi (rayukanmu sadaukarwa gare shi) kariya da taimakonsa, ya kasance tare da wannan al'umma.
Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah