IQNA – Da yawan jama’a sun taru a garin Nushabad mai cike da tarihi da ke kusa da Kashan a tsakiyar kasar Iran, domin halartar taron da ake kira Taziyeh na wanda ake nuna abin da ya faru da iylan gidan manzo, wanda taron ya gudana a ranar 7 ga Yuli, 2025.
Taron dai ya kunshi tunawa da shahadar Imam Husaini (AS) jikan Annabi Muhammad (SAW) da kuma irin wahalhalun da ‘yan uwa suka sha bayan yakin Karbala a shekara ta 680 miladiyya.