IQNA

UNRWA ta jaddada Bukatar Matsuguni na Gaggawa a zirin Gaza

17:15 - September 05, 2025
Lambar Labari: 3493822
IQNA - Hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ‘yan gudun hijira ta jaddada bukatar samar da matsuguni da gadaje da barguna da tantuna cikin gaggawa a zirin Gaza, inda ta yi nuni da cewa Falasdinawa a Gaza na fama da karancin kayan masarufi a karkashin hare-haren Isra’ila.

A cewar Anadolu, UNRWA ta bayyana cewa Falasdinawa a Gaza ba su da kayan masarufi a karkashin hare-haren Haramtacciyar Kasar Isra'ila tare da jaddada kiran da ta yi na a dage shingen da Isra'ila ta yi da ke hana shigar da kayan agaji.

A cikin wata sanarwa a dandalin sada zumunta na kamfanin X na Amurka, UNRWA ta ce: "An hana iyalai a Gaza kayayyakin masarufi, kuma ba a ba mu damar kai wani agaji ba tsawon watanni shida."

Sanarwar ta jaddada bukatar samar da matsuguni da gadaje da barguna da tantuna cikin gaggawa a Gaza tare da bayyana cewa hukumar a shirye take ta samar da su.

UNRWA ta kuma jaddada kiranta na kawo karshen killace yankin Zirin Gaza na tsawon watanni da Isra'ila ta yi, wanda ya hana kai agajin jin kai a yankin.

 

4303412

 

captcha