IQNA

Hare-Haren Isra'ila kudanci da gabashin kasar Lebanon

18:51 - January 11, 2026
Lambar Labari: 3494482
IQNA - Kafofin yada labaran kasar Lebanon sun bayar da rahotanni da ke cewa Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a yankuna daban-daban na kudanci da gabashin kasar.

Tashar Almayadeen ta bayar da cewa cewa, jiragen yakin  Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a yankuna daban-daban na kudanci da gabashin kasar Lebanon.

Wannan na zuwa ne a wani mataki daketa yarjejeniyar dakatar dabude wuta da aka cimmawa,wanda ya kallafawa Isra'ila dakatar da hare-harenta a kan kasar ta Lebanon.

Rahotannin sun karada cewa, hare-haren sun nufi yankuna da ke kudanci da suka hada da Qatrani,Mahmudiyya, Juzain da kecikin gundumar Tuffah a kudancin kasar Lebanon.

Haka nan kuma sun kai wasu hare-haren a yankin Beqaa, inda aka bayyana cewa an samu harar kaddarori,amma ba a bayar darahoton rasa rayuka ba.

A bisa wannan rahoto a cikin kasadasaoi 24 da suka gabata Isra'ila ta kai hare-hare sau 25 a kudancin kasar Lebanon.

 

4328107

captcha