
A eahoton da tashar Alalam ta bayar, Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi gargadi game da mawuyacin halin da mutane suke ciki a yankin zirin Gaza baki daya.
Rahoton ya ce bisa laakari da yanayin sanyin hunturu da ake a yankin,wannan yasa lamurra sun kara tazzara matuka,kasantuwar mutane suna rayuwa ba tare da abubuwan da za su basu kariya daga sanyi ba.
Baya ga haka kuma a cikin irin wannan hallin yahudawa suna ci gaba da kai hare-haren kisan kare dangi a yankin inda har yanzu suna kashe mutane kullum rana ta Allah.
Bugu da kari Hamas ta kara dacewa, gwamnatin yahudawa tana daukarv matakai na kara tsanata irin wannan hali da mutane suke ciki,musamman ta hanyar kawo tsaiko dacikas ga ayyukan shigar da kayan jin kai ga mutanen yankin.
4328485