IQNA

Bunkasa diflomasiyya dahadin kan musulunci tsakanin Iran da Malaysia

18:55 - January 22, 2026
Lambar Labari: 3494519
IQNA - Hojjatol Islam Shahriyari babban magatakardan cibiyar kusanto da mazhabobin musulunci tare da wasu malaman Ahlu sunnah na Iran sun gana da shugaban majalisar dokokin Malaysia.

Rahotanni sun ce babban magatakardan cibiyar kusanto da mazhabobin musulunci Hojjatol Islam Shahriyari tare da wasu malaman Ahlu sunnah na Iran sun gana da shugaban majalisar dokokin Malaysiada nufin kara karfafa hadin kai tsakanin bangarorin musulmi.

A yayion ganawar an tabo batutuwa dadama da suka zama a sahun gaba wajen muhimmanci ga al'ummar musulmi musamman a wannann zamani da ake ciki.

Mafi muhimmancin lamari shi ne hadin kai tsakanin dukkanin bangarori na musulmi sunna da sunnah da sauran bangarori da suke cikin addini,musamman bisa la'akari dakalubaledake gaban musulmia  halin yanzu.

baya ga haka kumaan tabo batun Falastinu wanda shi ne batu na farko a duniyar musulmi a yau da kuma tunanin yadda za a taimaka ma Falastinawa kan halin da suke ciki.

Hojjatol Islam Shahriyari ya tabo batun yanayin musulmi ahlu sunna wadanda su ne marasarinjayea  kasar Iran, inda yace suna da dukkanin hakkokin kamar kowane dan kasa,baya ga haka kuma ta fuskar gudanar da harkokinsu na addini suna da cikakken 'yanci,inda ya ce ahlu sunnah suna da masallaia sama da dubu 18 da makarantu 600 a cikin kasar.

 

4329730/

 

 

 

captcha