IQNA

Ahmad Nu’aina: Aikin Likitanci Bai Hana Ni Ayyukana A Bangaren Kur’ani Ba

0:00 - March 24, 2026
Lambar Labari: 3494770
IQNA - Fitaccen makarancin kur’ani kuma likita Dr. Ahmad Nu’aina ya bayyana cewa, aikinsa na likitanci bai taba hana shi harkokinsa a bangaren kur’ani ba.

A wata hira da aka yi yi da shi, Fitaccen makarancin kur’ani kuma likita Dr. Ahmad Nu’aina ya bayyana cewa, aikinsa na likitanci bai taba hana shi harkokinsa a bangaren kur’ani ba a rayuwarsa.

Ya ce tun yana karami ya tasirantu da lamarin kur’ani a kan hakan yak an halarci makarantar kur’ani da ma sauran dukkanin wurare da ake gudanar da tarukan kur’ania  garinsu.

Har lokacin day a kamala karatun sakadanre ya shiga jami’a, inda ya fara karatun likitancia  jami’a, amma kuma a lokaci guda yana ci gaba da sauran harkokinsa a bangaren kur’ani mai tsarki.

Ya ce wanda ya kowa masa karatun kur’ani wata malamar kur’ani ce mai suna Ummu Sa’ad a yankinsu, wadda take da makaranta ta musamamn domin koyar da karatun kur’ani.

Bayan ya zama cikakken likita ya ci gaba da aikinsa a asibitoci da sauran cibiyoyin kiwon lafiya domin yi wa marasa lafiya lafiya magani, amma kuma a kowace rana yana da lokutan karatun kur’ani da kuma halartar wurare tarukan kur’ani.

Ya ce a mafi yawan lokuta da yamma zuwa dare ne yake halartar wurare tarukan karatun kur’ani, inda shi aknsa yana daga cikin masu gabatar da kira’a a wuraren tarukan kur’ani na kasar Masar.

 

4341910

 

 

 

 

 

captcha